Luk 19:29-40 Littafi Mai Tsarki (HAU)

29. Da ya kusato Betafaji da Betanya, a wajen dutsen da ake kira Dutsen Zaitun, ya aiki almajiransa biyu,

30. ya ce musu, “Ku shiga ƙauyen can da yake gabanku. Da shigarku za ku ga wani aholaki a ɗaure, wanda ba a taɓa hawa ba. Ku kwanto shi.

31. Kowa ya tambaye ku, ‘Don me kuke kwance shi?’ ku ce, ‘Ubangiji ne yake bukatarsa.’ ”

32. Sai waɗanda aka aika suka tafi, suka tarar kamar yadda ya faɗa musu.

33. Suna cikin kwance aholakin, masu shi suka ce musu, “Don me kuke kwance aholakin nan?”

34. Sai suka ce, “Ubangiji ne yake bukatarsa.”

35. Sai suka kawo shi wurin Yesu. Da suka shimfiɗa mayafansu a kan aholakin, suka ɗora Yesu.

36. Yana cikin tafiya, sai mutane suka shisshimfiɗa mayafansu a hanya.

37. Da ya zo gab da gangaren Dutsen Zaitun, sai duk taron almajiran suka ɗauki murna, suna yabon Allah da murya mai ƙarfi saboda duk mu'ujizan da suka gani.

38. Suka ce, “Albarka ta tabbata ga Sarkin nan mai zuwa da sunan Ubangiji! Salama ta tabbata a Sama, ɗaukaka kuma ga Allah!”

39. Sai waɗansu Farisiyawa a cikin taron suka ce masa, “Malam, ka kwaɓi almajiranka mana!”

40. Ya amsa ya ce, “Ina dai gaya muku, ko waɗannan sun yi shiru, to, duwatsu ma sai su ɗauki sowa.”

Luk 19