43. Suka yi wa mutanen Biliyaminu tarko, suka runtume su ba tsayawa tun daga Menuha har zuwa daura da Gibeya daga gabas.
44. Aka kashe jarumawan mutanen Biliyaminu mutum dubu goma sha takwas (18,000).
45. Sauran suka juya, suka gudu, suka nufi wajen hamada zuwa Dutsen Rimmon. A kan hanyoyi, aka kashe musu mutum dubu biyar. Aka kuma runtumi sauran da suka ragu har zuwa Gidom inda suka kashe mutum dubu biyu.
46. Mutanen Biliyaminu da aka kashe a ran nan dubu ashirin da biyar (25,000) ne. Dukansu kuwa jarumawa ne.
47. Amma mutum Ι—ari shida suka juya, suka gudu suka nufi hamada zuwa Dutsen Rimmon inda suka zauna har wata hu:du.