L. Mah 19:1-2 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A lokacin nan ba sarki a Isra'ila. Sai wani Balawen da yake zama a wani lungu na ƙasar tudu ta Ifraimu ya ɗauko wata mace daga Baitalami ta Yahudiya ta zama ƙwarƙwararsa.

2. Ƙwarƙwarar kuwa ta ji haushinsa, ta koma gidan mahaifinta a Baitalami ta Yahudiya. Ta zauna a can har wata huɗu.

L. Mah 19