Sa'ad da suke ta farin ciki, sai suka ce, “A kawo Samson ya yi mana wasa.” Sai suka kawo Samson daga kurkuku, ya kuwa yi wasa a gabansu. Suka sa ya tsaya a tsakanin ginshiƙai.