L. Kid 7:1-12-83 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A ranar da Musa ya gama kafa alfarwa ta sujada, ya shafa mata mai, ya tsarkake ta, da dukan kayayyakinta, ya kuma shafa wa bagaden mai, ya tsarkake shi da dukan kayayyakinsa.

10. Sai shugabanni suka miƙa hadayu domin keɓewar bagade a ranar da aka zuba masa mai. Suka fara miƙa sadakokinsu a bagaden,

11. Ubangiji kuma ya ce wa Musa, “Bari shugabannin su kawo hadayunsa domin keɓewar bagade, har kwana sha biyu, kowa a ranarsa.”

12-83. Suka miƙa hadayunsu bi da bi kamar haka, Kabila Shugaba Yahuza Nashon ɗan Amminadab Issaka Netanel ɗan Zuwar Zabaluna Eliyab ɗan Helon Ra'ubainu Elizur ɗan Shedeyur Saminu Shelumiyel ɗan Zurishaddai Gad Eliyasaf ɗan Deyuwel Ifraimu Elishama ɗan Ammihud Manassa Gamaliyel ɗan Fedazur Biliyaminu Abidan ɗan Gideyoni Dan Ahiyezer ɗan Ammishaddai Ashiru Fagiyel ɗan Okran Naftali Ahira ɗan Enan Hadayun da kowannensu ya kawo duk daidai da juna suke, farantin azurfa na shekel ɗari da talatin, da kwanon azurfa na shekel saba'in, bisa ga ma'aunin kuɗin da ake aiki da shi, duka suna cike da garin da aka kwaɓa da mai domin hadaya ta gari, cokali na zinariya guda na shekel goma, cike da kayan ƙanshi, da ɗan bijimi guda, da rago ɗaya, da ɗan rago bana ɗaya domin hadaya ta ƙonawa, da akuya guda domin hadaya ta zunubi, da bijimai biyu, da raguna biyar, da awaki biyar, da 'yan raguna biyar bana ɗaya ɗaya, domin hadaya ta salama.

L. Kid 7