1. A ranar da Musa ya gama kafa alfarwa ta sujada, ya shafa mata mai, ya tsarkake ta, da dukan kayayyakinta, ya kuma shafa wa bagaden mai, ya tsarkake shi da dukan kayayyakinsa.
2. Sai shugabannin Isra'ila, wato shugabannin gidajen kakanninsu, su ne shugabannin kabilansu, waɗanda suka shugabanci waɗannan da aka ƙidaya,
3. suka kawo hadayarsu a gaban Ubangiji, karusai shida rufaffu, da takarkarai goma sha biyu. Shugabanni biyu suka ba da karusa ɗaya, kowannensu kuwa ya ba da takarkari ɗaya, da suka gama miƙa su,
4. sai Ubangiji ya ce wa Musa,
5. “Karɓi waɗannan daga gare su domin a yi aiki da su a alfarwa ta sujada. Ka ba da su ga Lawiyawa, a ba kowane mutum bisa ga aikinsa.”
6. Musa kuwa ya karɓi karusan, da takarkaran, ya ba Lawiyawa.
7. Ya ba 'ya'ya maza na Gershon karusai biyu da takarkarai huɗu bisa ga aikinsu.
8. Ya kuwa ba 'ya'ya maza na Merari karusai huɗu da takarkarai takwas bisa ga aikinsu, a hannun Itamar ɗan Haruna, firist.
9. Amma bai ba 'ya'ya maza na Kohat kome ba, domin aikinsu shi ne lura da kayayyaki masu tsarki waɗanda ake ɗauka a kafaɗa.
10. Sai shugabanni suka miƙa hadayu domin keɓewar bagade a ranar da aka zuba masa mai. Suka fara miƙa sadakokinsu a bagaden,