7. sai ya hurta zunubinsa, sa'an nan ya biya cikakkiyar diyyar abin da ƙarin humushin abin, ya ba mutumin da ya yi wa laifin.
8. Idan wanda ya yi wa laifin ya rasu, ba shi kuma da wani dangi na kusa wanda za a ba diyyar, sai a kai diyyar gaban Ubangiji domin firist, tare da ragon hadaya, don yin kafarar da za a yi masa.
9. Dukan sadakoki na tsarkakakkun abubuwa na Isra'ilawa waɗanda sukan kawo wa firist, za su zama nasa.
10. Kowane firist zai adana sadakokin da aka ba shi.