L. Kid 5:15-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. duk da haka sai mutum ya kawo matarsa a gaban firist, ya kawo kuma hadayar da ake bukata, wato humushin garwar garin sha'ir, amma kada ya zuba mai ko kayan ƙanshi, gama hadaya ce domin kishi, domin a bayyana gaskiya a fili.

16. Sai firist ya kawo ta kusa, ya tsai da ita a gaban Ubangiji.

17. Ya ɗebo ruwa mai tsarki a cikin kasko, ya kuma ɗauki ƙurar ƙasar da take a alfarwa ta alkawari ya zuba a ruwan.

18. Sa'an nan firist zai kwance gashin kanta, ya sa hadaya ta gari don tunawa a hannuwanta, hadayar gari ce ta kishi. Ya riƙe ruwan nan mai ɗaci da yake kawo la'ana a hannunsa.

19. Sa'an nan zai sa ta ta yi rantsuwa, ya ce mata, “Idan wani mutum bai kwana da ke ba, to, bari ki kuɓuta daga la'anar da ruwan nan mai ɗaci zai kawo.

20. Amma idan kin kwana da wani mutum wanda ba mijinki ba ne,

21. bari Ubangiji ya sa sunanki ya la'antu cikin jama'arki, ya sa cinyarki ta shanye, cikinki kuma ya kumbure.

L. Kid 5