L. Kid 33:9-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Suka tashi daga Mara suka zo Elim inda akwai maɓuɓɓugan ruwa guda goma sha biyu da itacen dabino guda saba'in. Sai suka sauka a can.

10. Suka tashi daga Elim, suka sauka a gefen Bahar Maliya.

11. Da suka tashi daga Bahar Maliya suka sauka a jejin Sin.

12. Suka tashi daga jejin Sin, suka sauka a Dofka.

13. Daga Dofka suka tafi Alush.

L. Kid 33