32. Za mu haye da shirin yaƙi a gaban Ubangiji zuwa cikin ƙasar Kan'aniyawa, amma za mu sami gādonmu a wannan hayin Urdun.”
33. Sa'an nan Musa ya ba Gadawa, da Ra'ubainawa, da rabin mutanen Manassa, ɗan Yusufu, mulkin Sihon, Sarkin Amoriyawa, da mulkin Og, Sarkin Bashan, wato ƙasar da biranenta da karkaransu.
34. Sai Gadawa suka gina Dibon, da Atarot, da Arower,
35. da Atarot-shofan, da Yazar, da Yogbeha,
36. da Bet-nimra, da Bet-aram su zama birane masu garu da shinge don dabbobi.
37. Ra'ubainawa kuwa suka gina Heshbon da Eleyale, da Kiriyatayim,
38. da Nebo, da Ba'al-meyon, da Sibma.
39. Mutanen Makir, ɗan Manassa, suka tafi Gileyad, suka ci ta da yaƙi, suka kori Amoriyawan da suke cikinta.
40. Sai Musa ya ba mutanen Makir, ɗan Manassa, Gileyad, suka zauna ciki.
41. Yayir, ɗan Manassa, ya tafi ya ci ƙauyukansu da yaƙi, suka ba su suna Hawot-yayir.
42. Noba kuma ya tafi ya ci Kenat da ƙauyukanta da yaƙi, ya ba ta suna Noba bisa ga sunansa.