1. Kabilan Ra'ubainu da Gad suna da dabbobi da yawa ƙwarai. Da suka ga ƙasar Yazar da ta Gileyad wuri ne mai kyau domin shanu,
2. sai suka je wurin Musa da Ele'azara firist, da shugabannin taron jama'ar,
3. suka ce, “Atarot, da Dibon, da Yazar, da Bet-nimra, da Heshbon, da Eleyale, da Simba, da Nebo, da Ba'al-meyon,
4. ƙasar da Ubangiji ya ci da yaƙi a gaban taron jama'a, ƙasa ce mai kyau don dabbobi. Ga shi kuwa, barorinka suna da dabbobi da yawa.
5. Idan mun sami tagomashi a gare ka, ka ba mu wannan ƙasa ta zama mallakarmu, kada ka kai mu a wancan hayin Urdun.”
6. Amma Musa ya amsa musu ya ce, “Wato sai 'yan'uwanku su yi ta yaƙi,ku kuwa ku yi zamanku a nan, ko?
7. Don me za ku karya zuciyar jama'ar Isra'ila daga hayewa zuwa ƙasar da Ubangiji ya ba su?
8. Haka iyayenku suka yi sa'ad da na aike su daga Kadesh-barneya don su dubo ƙasar.
9. Gama sa'ad da suka tafi Kwarin Eshkol suka ga ƙasar, suka karya zuciyar jama'a daga shigar ƙasar da Ubangiji ya ba su.