31. Musa da Ele'azara firist, suka yi yadda Ubangiji ya umarci Musa.
32. Yawan ganimar da sojoji suka kawo ke nan, tumaki dubu ɗari shida da dubu saba'in da dubu biyar (675,000),
33. shanu dubu saba'in da dubu biyu (72,000),
34. jakai dubu sittin da dubu ɗaya (61,000),
35. 'yan mata dubu talatin da dubu biyu (32,000) waɗanda ba su san namiji ba.
36. Kashin da aka ba sojoji waɗanda suka tafi yaƙi ne nan, tumaki dubu ɗari uku da talatin da bakwai da ɗari biyar (337,500).
37. Daga ciki aka fitar da tumaki ɗari shida da saba'in da biyar domin Ubangiji.
38. Shanu kuma dubu talatin da dubu shida (36,000), daga ciki aka fitar da shanu saba'in da biyu domin Ubangiji.
39. Jakai dubu talatin da ɗari biyar (30,500), daga ciki aka fitar da jakai sittin da ɗaya domin Ubangiji.