9. Mace wadda mijinta ya rasu ko sakakkiya, dole ta cika wa'adin da ta yi, da kowane alkawari, za su tabbata.
10. Idan macen aure ta yi wa'adi ko alkawari ba za ta yi wani abu ba,
11. idan mijinta ya ji, amma bai ce mata kome ba, to, sai wa'adinta da kowace irin rantsuwarta su tabbata.
12. Amma idan mijinta ya hana ta a ranar da ya ji, to, sai ta bari. Mijinta ya hana ta ɗaukar wa'adin, Ubangiji kuwa zai gafarce ta.
13. Mijinta yana da iko ya tabbatar, ko kuwa ya rushe kowane wa'adi da kowane irin alkawarin da ta ɗauka.
14. Idan mijinta ya yi shiru, bai ce mata kome ba, to, dole ta cika kowane abu da ta yi wa'adi da wanda kuma ta ɗauki alkawarinsa. Shirun da ya yi ya yardar mata.