5. Ubangiji ya ce wa Musa,
6. “Kawo kabilar Lawiyawa kusa, ka sa su su yi aiki tare da Haruna, firist.
7. Sai su yi wa firistoci da dukan jama'a aiki a gaban alfarwa ta sujada.
8. Su za su lura da kayayyakin alfarwa ta sujada su kuma yi wa Isra'ilawa aiki.
9. Abin da Lawiyawa za su yi, shi ne su yi wa Haruna da 'ya'yansa aiki.
10. Ka sa Haruna da 'ya'yansa maza, su kula da aikinsu na firist, idan kuwa wani mutum dabam ya yi ƙoƙarin yin wannan aiki, to, za a kashe shi.”
11. Ubangiji kuma ya ce wa Musa,
12. “Ga shi, na ɗauki Lawiyawa daga cikin Isra'ilawa a maimakon kowane ɗan farin da ya buɗe mahaifa daga cikin mutanen Isra'ila. Lawiyawa za su zama nawa.
13. Gama 'yan fari duka nawa ne, tun daga ranar da na kashe 'ya'yan fari na ƙasar Masar, na keɓe wa kaina duk ɗan fari na Isra'ila, na mutum da na dabba. Za su zama nawa, ni ne Ubangiji.”
14. Ubangiji ya yi magana da Musa a jejin Sinai, ya ce masa
15. ya ƙidaya mazaje na kabilar Lawi bisa ga gidajen kakanninsu da iyalansu, tun daga mai wata ɗaya zuwa gaba.
16. Haka Musa ya ƙidaya su bisa ga maganar Ubangiji, kamar yadda ya umarce shi.
17. Waɗannan su ne 'ya'yan Lawi, maza, bisa ga sunayensu, da Gershon, da Kohat, da Merari.
18. Waɗannan su ne sunayen 'ya'yan Gershon, maza, bisa ga iyalansu, Libni da Shimai.
19. Ga 'ya'yan Kohat, maza, bisa ga iyalansu, da Amram, da Izhara, da Hebron, da Uzziyel.