L. Kid 26:54-65 Littafi Mai Tsarki (HAU)

54. Za ka ba babbar kabila babban rabo, ka ba ƙaramar kabila ƙaramin rabo. Kowace kabila za a ba ta gādo bisa ga yawanta.

55. Amma za a rarraba musu gādon ƙasar kabila kabila ta hanyar kuri'a.

56. Za a rarraba gādo tsakanin manya da ƙananan kabilai ta hanyar kuri'a.”

57. Waɗannan su ne Lawiyawan da aka ƙidaya bisa ga iyalansu, Gershon, da Kohat, da Merari.

58. Sauran iyalin Lawiyawa daga zuriyar Libni ne, da Hebron, da Mali, da Mushi, da Kora. Kohat shi ne mahaifin Amram,

59. wanda ya auri Yokabed 'yar Lawi wadda aka haifa masa a Masar. Yokabed ta haifa wa Amram, Haruna, da Musa, da Maryamu, 'yar'uwarsu.

60. Haruna yana da 'ya'ya huɗu maza, Nadab, da Abihu, da Ele'azara, da Itamar.

61. Amma Nadab da Abihu sun mutu saboda sun miƙa hadaya da haramtacciyar wuta a gaban Ubangiji.

62. Mazan da aka ƙidaya daga mai wata guda zuwa gaba sun kai dubu ashirin da dubu uku (23,000). Ba a haɗa jimillarsu tare da ta sauran Isra'ilawa ba, da yake ba a ba su gādo tare da su ba.

63. Waɗannan su ne Isra'ilawa waɗanda Musa da Ele'azara, firist, suka ƙidaya a filayen Mowab wajen Kogin Urdun daura da Yariko.

64. Amma a cikin waɗannan da aka ƙidaya, ba wanda ya ragu daga Isra'ilawa waɗanda Musa da Haruna, firist, suka ƙidaya a jejin Sinai.

65. Gama Ubangiji ya riga ya yi magana a kansu, cewa lalle za su mutu a jeji. Ba wani mutumin da ya ragu daga cikinsu, sai dai Kalibu ɗan Yefunne, da Joshuwa ɗan Nun.

L. Kid 26