1. Da Sarkin Arad, Bakan'ane, wanda yake zaune a Negeb, ya ji Isra'ilawa suna zuwa ta hanyar Atarim, sai ya fita ya yi yaƙi da Isra'ilawa, ya kama waɗansu daga cikinsu.
2. Sai Isra'ilawa suka yi wa'adi ga Ubangiji, suka ce, “In hakika, za ka ba da mutanen nan a hannunmu, lalle za mu hallaka biranensu ƙaƙaf.”