1. Sai Ubangiji ya ce wa Haruna, “Kai da 'ya'yanka, da gidan mahaifinka za ku ɗauki hakkin abin da ya shafi alfarwa ta sujada. Kai da 'ya'yanka kuma za ku ɗauki hakkin aikinku wanda ya shafi firistoci.
2. Ka kawo 'yan'uwanka tare da kai, wato kabilar Lawi, kakanka, don su yi muku aiki sa'ad da kai da 'ya'yanka kuke gaban alfarwa ta sujada.