1. Ubangiji ya yi magana da Musa ya ce,
2. “Ka faɗa wa Isra'ilawa su ba ka sanduna, sanda guda daga kowane shugaban gidan kakanninsu, sanduna goma sha biyu ke nan. Ka rubuta sunan kowane mutum a sandansa.
3. Ka rubuta sunan Haruna a kan sandan Lawi, gama akwai sanda guda domin kowane gidan kakanninsu.
4. Sai ka ajiye su a alfarwa ta sujada a gaban akwatin alkawari, inda nakan sadu da kai.