L. Kid 14:12-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Zan kashe su da annoba, in raba su da gādonsu. Zan yi wata al'umma da kai, wadda za ta fi su girma da iko.”

13. Amma Musa ya ce wa Ubangiji, “Ai, Masarawa za su ji, gama ka fitar da mutanen daga cikinsu da ƙarfin ikonka.

14. Za su kuwa faɗa wa mutanen wannan ƙasa, gama sun riga sun ji, kai, ya Ubangiji, kana cikin tsakiyar jama'ar nan wadda kake bayyana kanka gare ta fuska da fuska. Girgijenka kuma yana tsaye a kansu, kakan kuma yi musu jagora da al'amudin wuta.

15. Idan kuwa ka kashe jama'ar nan gaba ɗaya, sai al'umman da suka ji labarinka, su ce,

16. ‘Domin Ubangiji ya kāsa kai jama'ar nan zuwa cikin ƙasar da ya rantse zai ba su, don haka ya kashe su a cikin jeji.’

17. Yanzu fa, ya Ubangiji, ina roƙonka ka sa ikonka ya zama da girma kamar yadda ka alkawarta cewa,

18. ‘Ubangiji mai jinkirin fushi ne, mai yawan ƙauna, kana gafarta mugunta da laifi, amma ba za ka ƙyale mai laifi ba, gama kakan ɗora wa 'ya'ya alhakin muguntar iyaye, har tsara ta uku da ta huɗu.’

19. Ina roƙonka ka gafarta muguntar wannan jama'a saboda ƙaunarka mai girma, kamar yadda kake gafarta musu tun daga Masar har zuwa yanzu.”

20. Sai Ubangiji ya ce, “Saboda maganarka na gafarta.

21. Amma, hakika, na rantse da zatina, kamar yadda ɗaukakata za ta cika duniya duka,

22. dukan mutanen da suka ga ɗaukakata da alamuna waɗanda na aikata a Masar, da kuma a jejin, suka kuwa jarraba ni har sau goma, ba su kuma yi biyayya da maganata ba,

23. ba za su ga ƙasar da na rantse zan ba kakanninsu ba. Duk waɗanda suka raina ni, ba za su ga ƙasar ba,

24. sai dai bawana Kalibu da yake ruhunsa dabam ne, gama ya bi ni sosai.

25. Yanzu fa, tun da yake Amalekawa da Kan'aniyawa suna zaune a kwarin, gobe sai ku juya ku nufi wajen jejin ta hanyar Bahar Maliya.”

L. Kid 14