32. Sai mutane suka tashi suka yi ta tattara makware dukan wannan yini, da dukan dare, har kashegari duka. Wanda ya tattara kaɗan, ya tara garwa metan. Suka shanya abinsu kewaye da zangon.
33. Tun suna cikin cin naman, sai Ubangiji ya husata da mutanensa, ya bugi jama'a da annoba mai zafi.
34. Don haka aka sa wa wurin suna Kibrot-hata'awa, wato makabarta, gama a can ne aka binne mutanen nan makwaɗaita.
35. Daga Kibrot-hata'awa mutanen suka yi tafiya zuwa Hazerot, a can suka sauka.