L. Fir 27:29-34 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3-7. Abin da aka ƙayyade za su biya bisa ga ma'aunin kuɗin da ake aiki da shi. Masu biya Abin da za su biya Maza masu shekara 20-60 Shekel hamsin Mata masu shekara 20-60 Shekel talatin Maza masu shekara 5-20 Shekel ashirin Mata masu shekara 5-20 Shekel goma sha biyar Maza masu wata guda zuwa shekara 5 Shekel biyar Mata masu wata guda zuwa shekara 5 Shekel uku Tsohon da ya fi shekara 60 Shekel goma sha biyar Tsohuwar da ta fi shekara 60 Shekel goma

29. Ko da mutum ne aka ba Ubangiji ɗungum, ba za a fanshe shi ba, sai a kashe shi.

30. Dukan ushirin amfanin ƙasar, ko na hatsi ne, ko na 'ya'yan itatuwa ne, na Ubangiji ne, gama tsattsarka ne ga Ubangiji.

31. Idan wani yana so ya fanshi ushiri na kowane iri, sai ya ƙara humushin tamanin ushirin.

32. Dukan ushiri na shanu, da na tumaki da awaki, duk dai dabbar da ta zama ta goma bisa ga ƙirgar makiyayan, keɓaɓɓiya ce, ta Ubangiji ce.

33. Ba ruwan kowa da kyanta ko rashin kyanta. Kada kuma a musaya ta. Idan kuwa an musaya ta, sai dai su zama tsarkakakku ga Ubangiji, ita da abar da aka yi musayar. Ba za a fanshe su ba.

34. Waɗannan su ne umarnan da Ubangiji ya ba Musa a kan Dutsen Sinai saboda isra'ilawa.

L. Fir 27