L. Fir 25:32-40 Littafi Mai Tsarki (HAU)

32. Amma a kan biranen Lawiyawa, da gidajen da suke cikin biranen da suka mallaka, Lawiyawa suna da izini su fanshe su a kowane lokaci.

33. Amma idan wani daga cikin Lawiyawa bai fanshi gidansa ba, a shekara ta hamsin ta murna sai a mayar masa da gidan nan na cikin birnin da suka mallaka, gama gidajen da suke cikin biranen Lawiyawa su ne nasu rabo a cikin Isra'ilawa.

34. Ba za a jinginar da hurumin biranensu ba, gama wannan shi ne abin mallakarsu har abada.”

35. “Idan ɗan'uwanka, Ba'isra'ile, ya talauce, ya kasa riƙon kansa, sai ka riƙe shi kamar baƙon da yake baƙunci a wurinka.

36. Kada ka ba shi rance da ruwa, amma ka ji tsoron Allah ka bar ɗan'uwanka, Ba'isra'ile, ya zauna tare da kai.

37. Kada ka ranta masa kuɗi da ruwa, kada kuma ka ba shi abinci don samun riba.

38. Ni ne Ubangiji Allahnku wanda ya fanshe ku daga ƙasar Masar don in ba ku ƙasar Kan'ana, in zama Allahnku.”

39. “Idan kuwa ɗan'uwanka, Ba'isra'ile, ya talauce har ya sayar da kansa gare ka, to, kada ka bautar da shi kamar bawa.

40. Amma ya zauna tare da kai kamar bara na ijara, ko kuwa kamar wanda yake baƙunci. Sai ya yi aiki tare da kai har shekara ta hamsin ta murna ta kewayo.

L. Fir 25