L. Fir 22:30-33 Littafi Mai Tsarki (HAU)

30. A ranar ce za a cinye, kada a bar kome ya kai gobe. Ni ne Ubangiji.

31. “Ku yi biyayya da umarnina. Ni ne Ubangiji.

32. Kada ku jawo wa sunana mai tsarki ƙasƙanci, amma sai mutanen Isra'ila su gane, ni mai tsarki ne. Ni ne Ubangiji na kuwa tsarkake ku,

33. na kuma fisshe ku daga ƙasar Masar domin in zama Allahnku. Ni ne Ubangiji.”

L. Fir 22