7. Kada firist ya auri karuwa, ko wadda mijinta ya sake ta, gama shi tsattsarka ne gare ni.
8. Dole jama'a su gan su da tsarki, gama suna miƙa hadaya ta ci gare ni. Ni ne Ubangiji, ni mai tsarki ne, na kuwa tsarkake mutanena.
9. 'Yar firist wadda ta ɓata kanta da yin aikin karuwanci, ta ƙasƙantar da mahaifinta, sai a ƙone ta da wuta.
10. “Firist wanda yake babba cikin 'yan'uwansa da aka zuba masa man keɓewa, aka kuma keɓe shi ya riƙa sa tufafin firist, kada ya bar gashin kansa buzu-buzu, ko kuwa ya kyakketa tufafinsa.
11. Kada ya kusaci gawa, ko gawar mahaifinsa, ko ta mahaifiyarsa don kada ya ƙazantu.
12. An keɓe shi domina, kada ya ƙazantar da kansa, kada kuwa ya ɓata alfarwa ta sujada ta wurin shiga gidan da gawa take, ko ta mahaifinsa, ko ta mahaifiyarsa ce.
13. Sai ya auri budurwa.