L. Fir 15:20-33 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. Duk abin da ta kwana a kai a lokacin rashin tsarkinta zai ƙazantu, haka kuma abin da ta zauna a kai zai ƙazantu.

21. Wanda kuma ya taɓa gadonta, sai ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, zai ƙazantu har maraice.

22. Haka kuma duk wanda ya taɓa kowane abin da ta zauna a kai, sai ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, zai ƙazantu har maraice.

23. Ko gado ne, ko kuma kowane abin da ta zauna a kai, sa'ad da wani ya taɓa shi zai ƙazantu har maraice.

24. Idan kuma wani ya kwana da ita, rashin tsarkinta zai shafe shi. Zai zama marar tsarki har kwana bakwai. Kowane gado da ya kwanta a kai zai ƙazantu.

25. Idan zubar jinin hailar macen ya yi kwanaki da yawa, ko kuwa kwanakin hailarta sun zarce ka'ida, a duk kwanakin zubar jininta za ta lizima cikin rashin tsarki daidai kamar lokacin hailarta.

26. Kowane gado da ta kwanta a kai a kwanakin zubar jininta, zai zama ƙazantacce, daidai kamar lokacin hailarta. Kowane abin da ta zauna a kai zai ƙazantu kamar a lokacin hailarta.

27. Wanda duk ya taɓa waɗannan abubuwa zai ƙazantu, sai ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, zai ƙazantu har maraice.

28. Bayan da hailarta ta tsaya, za ta ƙidaya kwanaki bakwai, bayan haka za ta tsarkaka.

29. A rana ta takwas sai ta kawo 'yan kurciyoyi biyu, ko 'yan tattabarai, a wurin firist a ƙofar alfarwa ta sujada.

30. Firist ɗin zai miƙa ɗaya hadaya don zunubi, ɗayan kuma don hadaya ta ƙonawa. Firist zai yi kafara dominta a gaban Ubangiji saboda rashin tsarkinta.

31. Ta haka za ka tsarkake jama'ar Isra'ila daga rashin tsarkinsu, domin kada su mutu saboda rashin tsarkinsu ta wurin ƙazantar da alfarwata wadda take tsakiyarsu.

32. Waɗannan su ne ka'idodi a kan wanda yake ɗiga, da wanda yake zubar da maniyyi, ƙazantacce ne.

33. Haka kuma wadda take haila, da kowane namiji ko mace, da yake ɗiga, da namijin da ya kwana da mace marar tsarki.

L. Fir 15