5. Amma idan 'ya mace ce ta haifa, za ta zama marar tsarki mako biyu kamar a kwanakin hailarta. Za ta ci gaba da zama cikin jinin har kwana sittin da shida.
6. Sa'ad da kwanakin tsarkakewarta na haihuwar ɗa ko 'ya suka cika, sai ta kai wa firist ɗan rago bana ɗaya, a ƙofar alfarwa ta sujada don hadaya ta ƙonawa, da ɗan tattabara, ko kurciya na yin hadaya don zunubi.
7. Sai ya miƙa ga Ubangiji, ya yi kafara dominta, za ta kuwa tsarkaka. Wannan shi ne abin da ya wajaba ga wanda ta haifi ɗa ko 'ya.