3. Gama kun mutu, ranku kuwa a ɓoye yake a gun Almasihu cikin Allah.
4. Sa'ad da Almasihu wanda yake shi ne ranmu ya bayyana, sai ku ma ku bayyana tare da shi a cikin ɗaukaka.
5. Saboda haka, sai ku kashe zukatanku ga sha'awace-sha'wacen duniya, wato fasikanci, da aikin lalata, da muguwar sha'awa, da mummunan buri, da kuma kwaɗayi, wanda shi ma bautar gumaka ne.
6. Saboda waɗannan abubuwa ne fushin Allah yake sauka a kan kangararru.
7. A dā kuna bin waɗannan sa'ad da suke jiki a gare ku.
8. Amma yanzu sai ku yar da duk waɗannan ma, wato fushi, da hasala, da ƙeta, da yanke, da alfasha.
9. Kada ku yi wa juna ƙarya, da yake kun yar da halinku na dā, da ayyukansa,
10. kun ɗauki sabon halin nan da ake sabuntawa ga sani, bisa ga kamannin Mahaliccinsa.
11. A nan kam, ba hanyar nuna bambanci a tsakanin Ba'al'umme da Bayahude, ko mai kaciya da marar kaciya, ko bare da baubawa, ko ɗa da bawa, sai dai Almasihu shi ne kome, shi kuma yake cikinmu duka.
12. Saboda haka, sai ku ɗauki halin tausayi, da kirki, da tawali'u, da salihanci, da haƙuri, idan ku zaɓaɓɓu ne na Allah, tsarkaka, ƙaunatattu,
13. kuna jure wa juna, in kuma wani yana da ƙara game da wani, sai su yafe wa juna. Kamar yadda Ubangiji ya yafe muku, ku kuma sai ku yafe.
14. Fiye da waɗannan duka, ku ɗau halin ƙauna, wadda dukkan kammala take ƙulluwa a cikinta.