K. Mag 30:9-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. don kada in wadata, har in yi musunka, in ce, “Wane ne Ubangiji?” Kada kuwa in yi talauci har in yi sata in saɓi sunan Allahna.

10. Kada ka kushe bara a wurin maigidansa domin kada ka yi laifin da zai sa a la'ance ka.

11. Akwai waɗansu mutane da sukan zagi iyayensu maza, ba sukan kuma nuna godiya ga iyayensu mata ba.

12. Akwai waɗansu mutanen da suke ganin kansu tsarkaka ne, alhali kuwa ƙazamai ne su.

13. Akwai waɗansu mutane da suke yi wa jama'a ƙallon raini suna ɗaurin gira.

14. Akwai waɗansu mutane waɗanda haƙoransu takuba ne, mataunansu kuma wuƙaƙe ne, don su cinye matalauta da masu fatara daga duniya.

17. Idan ɗa ya raina mahaifi, ya kuma yi wa mahaifiya ba'a hankakin kwari za su ƙwaƙule masa idanu, 'ya'yan mikiya za su cinye.

K. Mag 30