K. Mag 30:12-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Akwai waɗansu mutanen da suke ganin kansu tsarkaka ne, alhali kuwa ƙazamai ne su.

13. Akwai waɗansu mutane da suke yi wa jama'a ƙallon raini suna ɗaurin gira.

14. Akwai waɗansu mutane waɗanda haƙoransu takuba ne, mataunansu kuma wuƙaƙe ne, don su cinye matalauta da masu fatara daga duniya.

K. Mag 30