K. Mag 17:12-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Gara mutum ya gamu da beyar ta mata wadda aka kwashe mata kwiyakwiyanta, da ka gamu da waɗansu wawaye suna aikin dakikancinsu.

13. Idan ka sāka alheri da mugunta, ba za ka iya raba gidanka da mugunta ba, faufau.

14. Mafarin jayayya kamar ɓarkewa madatsar ruwa ne, sai a tsai da ita tun ba ta haɓaka ba.

15. Da wanda ya baratar da mugun da wanda ya kā da adali, duk abin ƙi suke ga Ubangiji.

16. Kashe kuɗi saboda ilimi ba shi da amfanin kome ga wawa, domin ba shi da tunani.

17. A ko yaushe abokai sukan nuna ƙaunarsu, 'yan'uwa kuma, ai, don su ɗauki nawayar juna suke.

18. Sai mutum marar tunani ne kaɗai zai ɗauki lamunin basusuwan maƙwabcinsa.

19. Shi wanda yake son zunubi, yana son wahala ke nan, wanda kuma yake yin fāriya a dukan lokaci yana neman tashin hankali ke nan.

K. Mag 17