5. Wauta ce mutum ya ƙi kulawa da abin da mahaifinsa ya koya masa, amma hikima ce idan ka karɓi tsautawarsa.
6. Adalai suna adana dukiyarsu, amma mugaye sukan rasa tasu dukiya sa'ad da wahala ta zo.
7. Mutane masu hikima suke yaɗa ilimi, amma banda wawaye.
8. Ubangiji yana murna sa'ad da adalai suke yin addu'a, amma yana ƙin hadayun da mugaye suke miƙa masa.
9. Ubangiji yana ƙin hanyoyin mugaye, amma yana ƙaunar mutumin da yake yin abin da yake daidai.
10. Idan ka yi abin da ba daidai ba, za ka sha hukunci sosai, za ka mutu idan ka ƙi yarda da tsautawa.