K. Mag 15:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Amsa magana da tattausan harshe takan kwantar da hasala, amma magana da kakkausan harshe takan kuta fushi.

2. Sa'ad da mai hikima ya yi magana yakan sa ilimi ya yi bansha'awa, amma wawaye sukan yi ta sheƙa rashin hankali.

3. Ubangiji yana ganin abin da yake faruwa a ko'ina, yana lura da mu, ko muna aikata alheri ko mugunta.

4. Kalmomin alheri suna kawo rai, amma maganganun ƙiyayya suna karya zuciyar mutum.

5. Wauta ce mutum ya ƙi kulawa da abin da mahaifinsa ya koya masa, amma hikima ce idan ka karɓi tsautawarsa.

K. Mag 15