27. Dabbobi da kayayyaki na birnin kaɗai Isra'ilawa suka kwashe ganima bisa ga faɗar Ubangiji zuwa ga Joshuwa.
28. Haka fa Joshuwa ya ƙone Ai, ya maishe ta tsibin kufai har abada. Tana nan haka har wa yau.
29. Ya rataye Sarkin Ai a bisa itace har maraice. Sa'ad da rana take faɗuwa Joshuwa ya umarta su ɗauke gawarsa daga itacen, su jefa a ƙofar birnin, su tsiba duwatsu da yawa a kanta. Tsibin duwatsun yana nan har wa yau.
30. Joshuwa ya gina wa Ubangiji Allah na Isra'ilawa bagade a bisa Dutsen Ebal.
31. Ya gina shi kamar yadda Musa bawan Ubangiji ya umarci Isra'ilawa, gama haka aka rubuta cikin Attaura ta Musa, aka ce, “Bagaden da aka yi da duwatsun da ba a sassaƙa ba, waɗanda ba mutumin da ya taɓa sa musu guduma.” A bisansa suka miƙa hadayu ta ƙonawa ga Ubangiji, da hadayu na salama.
32. A nan, a idon Isra'ilawa, Joshuwa ya kafa dokokin Musa a bisa duwatsun.
33. Sai Isra'ilawa duka, baƙi da haifaffun gida, tare da dattawansu da shugabanninsu, da alƙalansu, suka tsaya daura da akwatin alkawari, suna fuskantar firistoci, wato Lawiyawa, waɗanda suka ɗauki akwatin alkawari na Ubangiji. Rabin mutanen suka tsaya a gaban Dutsen Gerizim, rabinsu kuma suka tsaya a gaban Dutsen Ebal kamar yadda Musa, bawan Ubangiji, ya riga ya umarta, cewa su sa wa jama'ar Isra'ila albarka.
34. Bayan haka ya karanta dukan zantuttukan shari'a, da na albarka da na la'ana, bisa ga dukan abin da aka rubuta cikin Attaura.