Josh 3:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Joshuwa kuwa ya tashi da sassafe, da shi da dukan jama'ar Isra'ila, suka kama hanya daga Shittim zuwa Urdun, inda suka sauka kafin su haye.

2. Bayan kwana uku sai shugabannin jama'a suka bibiya zango,

3. suna umartar jama'ar suna cewa, “Sa'ad da kuka ga akwatin alkawari na Ubangiji Allahnku, sai ku tashi daga inda kuke, ku bi shi,

4. domin ku san hanyar da za ku bi, gama ba ku taɓa bin hanyar ba. Sai dai tsakaninku da shi za ku bar rata misalin nisan kamu dubu biyu, kada ku kusace shi.”

5. Sai Joshuwa ya ce wa jama'a, “Ku tsarkake kanku, gama gobe Ubangiji zai aikata abin al'ajabi a tsakiyarku.”

14-15. (Da kaka Urdun yakan yi cikowa makil.) Jama'a fa, suka tashi daga alfarwansu don su haye Urdun. Firistocin da suke ɗauke da akwatin alkawari suna gaba. Da firistocin suka tsoma ƙafafunsu cikin ruwa daga gefe,

Josh 3