22. Joshuwa kuma ya ce wa mutanen, “Ku ne shaidun kanku da kanku, kun zaɓi Ubangiji don ku bauta masa.”Sai suka ce, “I, mu ne shaidu.”
23. Joshuwa ya ce, “To, ku kawar da gumakan da suke cikinku, ku sa zuciyarku ga Ubangiji, Allah na Isra'ila.”
24. Jama'a suka ce wa Joshuwa, “Za mu bauta wa Ubangiji Allahnmu, za mu kuma yi biyayya da muryarsa.”
25. A wannan rana, Joshuwa ya yi alkawari da jama'a a Shekem, ya kafa musu dokoki da ka'idodi.
26. Ya kuwa rubuta waɗannan kalmomi a littafin Shari'ar Ubangiji. Ya kuma ɗauki wani babban dutse, ya kafa a ƙarƙashin itacen oak a wuri mai tsarki na Ubangiji.
27. Sai ya ce wa jama'a, “Wannan dutse shi ne shaida a kanmu, gama ya ji dukan abin da Ubangiji ya faɗa mana, domin haka zai zama shaida a kanku, don kada ku yi wa Allahnku ƙarya.”
28. Joshuwa kuwa ya sallami jama'ar, kowane mutum ya koma wurin gādonsa.
29. Bayan waɗannan al'amura, sai Joshuwa ɗan Nun, bawan Ubangiji, ya rasu yana da shekara ɗari da goma da haihuwa.
30. Suka binne shi a ƙasar gādonsa a Timnat-sera wadda take cikin karkarar tuddai ta Ifraimu, arewa da dutsen Ga'ash.