14. “A yanzu ina gaba da bin hanyar da kowa a duniya yakan bi, ku duka kuwa, a zukatanku da rayukanku, kun sani dukan abubuwan alheri da Ubangiji Allahnku ya alkawarta muku sun tabbata, ba ɗayan da bai tabbata ba.
15. Amma kamar yadda Ubangiji Allahnku ya cika alkawaran da ya yi muku, haka nan kuma Ubangiji zai aukar muku da masifu, har ya hallaka ku daga ƙasan nan mai albarka da Ubangiji Allahnku ya ba ku.
16. Lokacin da kuka karya alkawarin Ubangiji Allahnku da ya umarce ku, kuka tafi kuka bauta wa gumaka, kuka sunkuya musu, to, Ubangiji zai yi fushi da ku, zai kuwa hallaka ku daga ƙasa mai albarka da aka ba ku.”