10. Zuriyar Haruna tana cikin iyalan Kohatawa waɗanda suke Lawiyawa. Kuri'arsu ce ta fito da farko.
11. Sai aka ba su Kiriyat-arba, wato Hebron, a ƙasar tuddai ta Yahuza tare da wuraren kiwo nata da suke kewaye. Arba shi ne mahaifin Anak.
12. Amma saurukan birnin da ƙauyukansu an ba Kalibu, ɗan Yefunne, su zama mallakarsa.
13. Biranen da aka ba zuriyar Haruna firist ke nan, Hebron tare da wuraren kiwo nata, ita kuwa birnin mafaka ce saboda wanda ya yi kisankai, da Libna tare da wuraren kiwo nata,
14. da Yattir tare da wuraren kiwo nata, da Eshtemowa tare da wuraren kiwo nata,