Daga can iyakar ta yi kudu, ta nufi cibiyar Luz, wato Betel, ta gangara zuwa Atarot-addar a bisa dutsen da yake kudu da Bet-horon ta kwari.