Josh 13:2-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Wannan ita ce ƙasar da ta ragu, dukan ƙasar Filistiyawa, da ta Geshuriyawa,

3. daga Shihor da yake gabas da Masar zuwa iyakar Ekron a wajen arewa. Wannan ƙasa ta Kan'aniyawa ce. Akwai ƙasar sarakuna biyar na Filistiyawa da yake a Gaza, da Ashdod, da Ashkelon, da Gat, da Ekron, da ƙasar Awwiyawa,

4. da dukan ƙasar Kan'aniyawa a wajen kudu, da Meyara ta Sidoniyawa, zuwa Afek, har zuwa iyakar Amoriyawa,

5. da ƙasar Gebaliyawa, da dukan Lebanon wajen gabas daga Ba'al-gad a gindin Dutsen Harmon zuwa iyakar Hamat,

6. da dukan mazaunan ƙasar tuddai, tun daga Lebanon zuwa Misrefot-mayim har da dukan Sidoniyawa. Ni da kaina zan kore su a gaban jama'ar Isra'ila. Kai kuwa za ka raba wa Isra'ilawa ƙasar ta zama gādonsu kamar yadda na umarce ka.

7. Yanzu fa sai ka raba wa kabilai tara da rabi ɗin nan ƙasar ta zama gādonsu.”

Josh 13