21. A wannan lokaci kuwa Joshuwa ya tafi ya hallaka Anakawa, wato gwarzayen nan da suke ƙasar tuddai, da Hebron, da Debir, da Anab, da dukan ƙasar tuddai ta Yahuza, da dukan ƙasar tuddai ta Isra'ilawa. Joshuwa ya hallaka su sarai duk da biranensu.
22. Babu wani gwarzon da ya ragu a ƙasar mutanen Isra'ila, sai a Gaza, da Gat, da Ashdod kaɗai ne waɗansunsu suka ragu.
23. Haka nan kuwa Joshuwa ya ci dukan ƙasar yadda Ubangiji ya faɗa wa Musa. Ya kuwa ba da ƙasar gādo ga Isra'ilawa kabila kabila. Ƙasar kuwa ta shaƙata da yaƙi.