16. Su kuwa suka amsa wa Joshuwa, suka ce, “Iyakar abin da ka umarce mu za mu yi, duk inda ka aike mu kuma za mu tafi.
17. Kamar yadda muka yi wa Musa biyayya a kowane abu haka nan za mu yi maka biyayya, Ubangiji Allahnka dai ya kasance tare da kai kamar yadda ya kasance tare da Musa.
18. Duk wanda ya ƙi bin umarninka, bai kuwa yi biyayya da maganarka da dukan irin abin da ka umarce shi ba, za a kashe shi. Kai dai ka dāge, ka yi ƙarfin hali.”