Josh 1:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Bayan rasuwar Musa, bawan Ubangiji, Ubangiji ya ce wa Joshuwa ɗan Nun, wanda ya yi wa Musa aiki,

2. “Bawana Musa ya rasu, sai ka tashi ka haye Kogin Urdun, kai da dukan jama'an nan, zuwa cikin ƙasar da nake ba Isra'ilawa.

3. Duk inda tafin sawunku ya taka na riga na ba ku, kamar yadda na alkawarta wa Musa.

Josh 1