1. Ba sauran baƙin ciki ga wadda take shan azaba. Dā an ƙasƙantar da ƙasar kabilan Zabaluna da na Naftali, amma nan gaba wannan jiha za ta sami daraja, tun daga Bahar Maliya, zuwa gabashin ƙasar a wancan sashe na Urdun, har zuwa Galili kanta, wurin da baƙi suke zaune.
2. Jama'ar da suka yi tafiya cikin duhu,Sun ga babban haske!Suka zauna a inuwar mutuwa,Amma yanzu haske ya haskaka su.
3. Ka ba su babbar murna, ya Ubangiji,Ka sa su yi farin ciki.Suna murna da abin da ka aikata,Kamar yadda mutane suke murna sa'ad da suke girbin hatsi,Ko sa'ad da suke raba ganima.