Ish 7:14-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Yanzu fa, Ubangiji kansa zai ba ku alama. Wata budurwa wadda take da ciki, za ta haifi ɗa, za a raɗa masa suna Immanuwel.

15. In ya yi girma har ya isa yanke shawara don kansa, madara da zuma ne abincinsa.

16. Kafin lokacin ya yi, ƙasashen sarakunan nan biyu waɗanda suka firgita ku za su zama kango.

17. “Ubangiji zai aukar maka da kwanakin wahala, kai da jama'arka, da dukan iyalin gidan sarauta, waɗanda suka fi muni tun lokacin da aka raba mulkin Isra'ila daga na Yahuza. Zai kawo Sarkin Assuriya!

18. “A lokacin nan, Ubangiji zai yi feɗuwa ya kirawo Masarawa su zo kamar ƙudaje daga manisantan mazaunan Kogin Nilu, ya kuma kirawo Assuriyawa su zo daga ƙasarsu kamar ƙudajen zuma.

19. Za su zo jingim su mamaye kwazazzabai da kogwanni cikin duwatsu, za su rufe kowane fili mai ƙayayuwa da kowace makiyaya.

20. “A lokacin nan, Ubangiji zai yi ijara da wanzami daga wancan hayi na Yufiretis, wato Sarkin Assuriya! Zai aske gyammanku, da gashin kawunanku, da na jikunanku.

Ish 7