Ish 7:14-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Yanzu fa, Ubangiji kansa zai ba ku alama. Wata budurwa wadda take da ciki, za ta haifi ɗa, za a raɗa masa suna Immanuwel.

15. In ya yi girma har ya isa yanke shawara don kansa, madara da zuma ne abincinsa.

16. Kafin lokacin ya yi, ƙasashen sarakunan nan biyu waɗanda suka firgita ku za su zama kango.

Ish 7