1. Wane ne wannan da yake zuwa daga Bozara cikin Edom? Wane ne wannan da ya sha ado da jajayen kaya, yana tafe, ga shi kuwa ƙaƙƙarfa?Ubangiji ne, mai ikon yin ceto, yana zuwa ya yi sanarwar nasara.
2. Me ya sa tufafinsa suke da ja haka, kamar na mutumin da ya tattake 'ya'yan inabi domin ya sami ruwan inabi?
3. Ubangiji ya amsa ya ce, “Na tattake al'ummai kamar 'ya'yan inabi, ba kuwa wanda ya taimake ni. Na tattake su cikin fushina, jininsu kuwa ya fantsamar wa dukan tufafina.
4. Na ga lokacin da zan fanshi mutanena ya yi, lokaci ne da zan hukunta wa abokan gābansu.
5. Na yi mamaki sa'ad da na duba, sai na ga ba wanda zai taimake ni. Amma fushina ya sa na sami ƙarfi, har ni kaina na ci nasara.
6. Da fushina na tattake dukan sauran al'umma, na farfashe su. Na kwararar da jinin ransu a ƙasa.”
7. Zan faɗi ƙaunar Ubangiji marar ƙarewa,Zan yabe shi saboda dukan abin da ya yi mana.Ya sa wa jama'ar Isra'ila albarka mai yawa,Saboda jinƙansa da ƙaunarsa marar matuƙa.
8. Ubangiji ya ce, “Su mutanena ne, ba za su ruɗe ni ba.” Saboda haka kuwa ya cece su
9. daga dukan wahalar da suke sha. Ba mala'ika ne ya cece su ba, amma Ubangiji ne. Da ƙaunarsa da juyayinsa ya fanshe su. A koyaushe yake lura da su a dā,