Ish 60:7-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Dukan tumaki na Kedar da Nebayot,Za a kawo miki su hadaya,A kuwa miƙa su a kan bagade domin Ubangiji ya ji daɗi.Ubangiji zai darajanta Haikalinsa fiye da dā.

8. Waɗannan jiragen ruwa fa? Suna tafe kamar gizagizai,Kamar kurciyoyi suna komowa gida.

9. Jiragen ruwa ne suke zuwa daga manisantan ƙasashe,Suna kawo mutanen Allah gida.Suna tafe da azurfa da zinariya,Domin su girmama sunan Ubangiji,Allah Mai Tsarki na Isra'ila,Wanda ya sa dukan al'ummai su girmama mutanensa.

10. Ubangiji ya ce wa Urushalima,“Baƙi ne za su sāke gina garukanki,Sarakunansu kuma za su bauta miki.Na hukunta ki da fushina,Amma yanzu zan nuna miki alheri da jinƙai.

11. Ƙofofinki za su kasance a buɗe dare da rana,Domin sarakunan al'ummai su kawo miki dukiyarsu.

12. Amma al'umman da ba su bauta miki ba,Za a hallakar da su.

Ish 60