5. zan ba ku matuni da suna a Haikalina da cikin garukana, da sun fi na 'ya'ya mata da maza. Zan ba ku tabbataccen suna wanda ba za a raba ku da shi ba.”
6. Ubangiji ya ce wa baƙin da suka bi shi, don su yi masa hidima, suna ƙaunar sunansa, sun kuma zama bayinsa, dukan wanda yake kiyaye ranar Asabar, bai kuwa ɓata ta ba, ya kuma cika alkawarinsa da aminci,
7. “Zan kai ku tsattsarkan dutsena, in sa ku yi murna a masujadata. Hadayunku na ƙonawa da sadakokinku za su zama abin karɓa a bagadena. Za a kira Haikalina wurin yin addu'a na dukan jama'a.”
8. Haka Ubangiji Allah, shi wanda ya tattara Isra'ilawa korarru, ya faɗa, ya ce, “Zan ƙara tattaro waɗansu, bayan waɗanda na riga na tattara.”
9. Dukanku namomin jeji ku zo ku ci, dukanku namomin jeji.