8. Ubangiji ya ce wa jama'arsa,“Idan lokacin da zan cece ku ya yi, zan nuna muku alheri.Zan ji kukanku in taimake ku.Zan tsare ku in kiyaye ku,Zan kuwa yi wa dukan mutane alkawari ta wurinku.Zan bar ku ku sāke zama a ƙasarku wadda take kufai a yanzu.
9. Zan ce wa 'yan kurkuku, ‘Ku tafi na sake ku!’Waɗanda suke cikin duhu kuwa, in ce musu,‘Ku fito zuwa wurin haske!’Za su zama kamar tumakin da suke kiwo a tuddai,
10. Ba za su taɓa jin yunwa ko ƙishi ba.Ba za su sha zafin rana da na hamada ba,Gama wanda yake ƙaunarsu ne zai bi da su.Zai bi da su zuwa maɓuɓɓugan ruwa.