Ish 46:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. “Wannan ne ƙarshen allolin Babila!Dā ana yi wa Bel da Nebo sujada,Amma yanzu ana labtunsu a kan jakuna,Sun zama nawaya a kan dabbobin da suka gaji!

2. Wannan ne ƙarshen waɗannan alloli,Gumaka ba su iya ceton kansu,Aka kame su aka tafi da su.

3. “Ku kasa kunne gare ni ku zuriyar Yakubu,Dukanku, mutanena da kuka ragu.Ina ta lura da ku tun daga lokacin da aka haife ku.

4. Ni ne Allahnku, zan kuwa lura da ku,Har lokacin da kuka tsufa kuka yi furfura.Ni na halice ku zan kuwa lura da ku,Zan yi muku taimako in kuwa kuɓutar da ku.”

5. Ubangiji ya ce, “Da wane ne za ku kwatanta ni?Akwai wani mai kama da ni?

6. Mutane suka buɗe alabensu suna zazzage zinariya,Suna auna azurfa a kan ma'auni.Suka yi jingar maƙerin zinariya don ya yi musu gunki,Sa'an nan suka rusuna suka yi masa sujada!

7. Suka ɗauke shi a kafaɗunsu su tafi da shi,Suna ajiyewa a wani wuri, ya yi ta tsayawa a can,Ba ya iya motsawa daga inda yake.Idan wani ya yi addu'a gare shi, ba zai iya amsawa ba,Ko ya cece shi daga bala'i.

8. “Ku tuna da wannan, ku masu zunubi,Ku dubi irin abin da na yi.

Ish 46